Yara kan Mata Yan Jihar Yobe Da Suka Yi Bajinta Tare kara Daga Darajar Najeriya A Duniya
Yara Yan Mata Yan Jihar Yobe Da Suka Yi Bajinta Tare kara Daga Darajar Najeriya A Duniya
Nafisa, Ruƙayya, da Khadija, yara ne ƴan mata masu hazaƙa ƴan asalin Jihar Yobe da suka yi bajinta tare da ƙara ɗaga darajar Najeriya a Duniya kwana-kwanan nan a birnin Landan na ƙasar Ingila.
A bayanan da Dokin Ƙarfe TV ta tattara, yara matan su uku sun haɗa da:
1. Nafisa Mohammad Sani, ƴar kimanin shekaru (17), wacce ta nuna tsantsar hazaƙa, zalaƙa, da ƙwarewar da ta fito da ita Duniya ta santa ta kuma yaba da bajintarta.
2. Ruƙayya Muhammad Fema, ƴar kimanin shekaru (15), yarinya ce zaƙaƙura, mai hikima da kaifin basira ta ja hankalin Duniya ta hanyar zama gwarzuwar da ta lashe gasar muhawara, lamarin da ya zama kanun labarai a Duniya.
3. Khadija Kashim Kalli, ba wata sananniya ce kafin wannan lokaci ba, amma yanzu haka ta samu nasarar lashe kambun hazaƙa na Duniya, hakan ya ba ta damar samun shahara da jinjina a Duniya.
Tuni gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni ta yaba da ƙwazon nasu tare da shirin karrama su gaba ɗaya kan wannan bajinta domin ƙarfafa musu gwiwa da ƙarin zaburar wa ga sauran yara.