Uncategorized

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya raba kyautar shinkafa buhu dubu

Masha Allah tabarakallah yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari mai dadi inda babban shehin malamin addinin musulunci daga jihar bauchi arewacin Nigeriya yayiwa talakawa goma ta arziki a cikin wannan yanayin kunci talauci da fatara fitaccen marubuci mai amfani da kafar sada zumunta.

Babban Malaminmu na Sunnah a jihar Bauchi Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya raba kyautar shinkafa Buhu dubu daya a kofar gidansa dake Dutsen Tanshi Bauchi wa mabukata kyauta

Kuma ba wannan karon bane Malam ya saba irin wannan kyauta domin ya kyautatawa mabukata dake unguwarsa a Bauchi.

Malam Ahmad Tijjani Guruntum dan kasuwa ne, ba dan siyasa bane, baya karban kudin ‘yan siyasa ya musu talle, amma ku dubi yadda yake taimakon jama’a da dukiyarsa.

Na tabbata Wallahi akwai Malaman da sun ninkashi a dukiya, akwai ‘yan siyasa da sun ninkashi a dukiya amma basuyi irin abinda yake yi ba wajen taimakon al’ummah, duniya kawai suka sa a gaba

A wannan yanayin da muke ciki Wallahi akwai mabukata, ‘yan uwa Musulmi suna kwana da yunwa suna bukatar a taimakesu, tabbas da Malamai masu arziki musamman wadanda suke karban kudi a gurin ‘yan siyasa zasu ware wani abu daga dukiyarsu su taimaki mabiyansu kamar wannan to da an samu sauki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button