Kannywood
Shahararren Dan Kasuwar Nan Alhaji Dahiru Mangal Ya Gwangwaje Mawaki Rarara Kyautar Sabuwar Mota
Attajirin Ɗan kasuwa ɗan asalin jihar Katsina Shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air Alhaji Ɗahiru Mangal ya baiwa mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Kyautar sabuwar mota ƙirar “Benz bayan Kona mashi gida da motoci Da wasu matasa bata gari sukai a Jihar Kano.
Wannan dai bashi ne karo na Farko ba da Mawaki ya samu kyautar Mota wanda hakan ya biyo bayan kone masa Gida da motoci da akayi a jahar kano a yayin da ake murmur lashe zaben Abba gida gida.