Jarumin Aminu Shariff (Momoh) yace abubuwan da ya sa wasu Jaruman Kannywood ke talaucawa bayan sun yi tashe.
Jarumin Aminu Shariff (Momoh) yace abubuwan da ya sa wasu Jaruman Kannywood ke talaucawa bayan sun yi tashe.
Wasu jaruman Kannywood da dama kan talauce ko su faɗa wanu hali na buƙatar taimako bayan sun ɗauki dogon lokaci suna tashe a masana’antar.
To sai dai wasu jaruman masana’antar sun ce rashin tsari da tanadi daga wasu jaruman ne ke haddasa musu faɗawa ƙangin talaucin.
A tattaunawarsu da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, Aminu Sheriff da ka fi sani da Momoh da kuma Bashir Bala Chiroki sun bayyana abubuwan da suke ganin ke haddasa matsalar.
Bashir Bala Chiroki – wanda a shekarun baya ya yi tashe, a yanzu kuma yake fama da rayuwa, inda har ya koma sana’ar sayar da kunun aya – ya ce abin da ke haddasa matsalar shi ne rashin tanadi da tsari mai kyau.
A nasa bangare, Aminu Sheriff Momoh, ya ce yana kallon matsalar ta fuskoki uku, da farko ya ce ya danganta da yadda jarumi ya ɗauki sana’ar film, ‘’shin ya ɗauke ta ne a matsayin sana’a ko kuwa wani abu na nishaɗi da zai zo ya yi, ya kuma kama gabansa idan an kammala’’
‘’Abu na biyu shi ne wacce irin rayuwa ya shirya wa kansa, ya ɗauki rayuwar ne da irin ɗaukakar da ya samu masana’antar, ma’ana ya fita daga wani rukuni na mutane ya koma wani?
Zai canja sutura da muhalli da ƙara kuɗin da yake kashewa ko kuma zai zauna a yadda yake?
Abu na uku shi ne wane shiri ya yi wa kansa zuwa rayuwarsa ta gaba, ‘’tun da dai ita ɗaukaka zuwa take yi kuma ta tafi, shin akwai wani tanadi da ya shirya wa rayuwarsa na yadda zai ɗora bayan gushewar ɗaukakar da ya samu a masana’antar’’, in ji Momoh.
Ya ce waɗannan su ne abubuwan da duk wani jarumi ya kamata ya yi la’akari da su bayan shigarsa Kannywood.
Ya ci gaba da cewa akwai jaruman da idan suna kan ganiyar ɗaukaka sai su dora wa kansu girman kai da ƙarya na sai sun canja matsayin da suke.
”Za ka ga mutum sai ya ce ruwa ma sai na gora zai sha, kuma ba zai ci abinci mai araha ba, sai mai tsada, ko ya riƙe babbar waya, ko babbar mota ko babban gida, wani ma sai ya biya kuɗi masu yawa ya kama hayar babban gida kawai saboda shi ya samu ɗaukaka”, in ji jarumin.



