Entertainment
Maimuna Kiyi Hakuri Wakar Da Kikaji An Sa A Wajan Biki
Maimuna Kiyi Hakuri Wakar Da Kikaji An Sa A Wajan Biki Na Ba Dake Nake Ba, Cewa Mawakí Ado Gwanja
Bayan fitar wata waƙa ta Ado Gwanja a lokacin bikin sa, mai suna sai yanzu nai Aure, mawakin yabi tsohuwar matar sa yana bata hakuri kan wakar, yace bada ita yake ba.
Yace tun kafin Auren su wakar take, a cewar sa tun muna tare kin sha jin wakar amma ban sake ta ba, yanzu ma bansan DJ yana da ita ba kawai Naji an kunna, ba yadda na iya, tunda bazan iya yin faɗa ranar Aure na ba.
Alamu suna nuna har yanzu akwai ƙauna tsakanin Gwanja da tsohuwar matar sa
Meye ra’ayin ku?



