Labarai

Innalillahi Ta Kashe Mijin Kawarta Bayan Ya Kama Su Dumu Dumu Suna Madigo A Cikin Gidan Sa

Ana zargin wata ta kashe mijin kawarta da wuka saboda yake kama su suna aikata mummunan aiki a cikin gidan sa ita da matar shi, wannan abu ya faru ne a wani kauyen jihar anambra.

Mijin da aka kashe ya kasance yana aiki ne a kwalegin lafiya dake wannan kauye na jihar anambra, sannan an kashe shine bayan ya dawo gida daga aiki lokacin ya tarar da matar da ita kan gado.

Matar shi ta samu damar guduwa bayan da taga mijin na ta ya fadi kasa cikin jini bayan da kawarta ta suka masa wannan wuka. Har yanzu ba’a gano inda take ba amma jami’ai iya kokarinsu.

Mutane sun tabbatar da mijin wanda aka kashe bashi da masaniyar matar shi ta dade tana wannan harka. Yan sanda sun tabbatar da kisan sannan sun kama wacce tayi yanzu haka tana hannun su.

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button